Hotuna: An kama mata da maza 2 masu satar mutane yansanda sun rushe gidansu a Kano


Yan sandan jihar Kano sun damke wata mata tare da wasu mutane biyu bisa zargin satar mutane domin karbar kudin fansa.


Wadanda aka kama sun hada da Maryam Muhammed mai shekara 23, Sani Ibrahim mai shekara 35 da Shamsuddeen Suleiman mai shekara 21.


An kama wadanda ake zargin ne a unguwar Jaba da ke karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, kuma ba tare da bata lokaci ba yansanda suka rushe gidan wadanda ake zargin bayan sun gano tarin makamai a gidan.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN