Gwamna Matawalle ya caccaki sarkin Anka


Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya tuhumci wasu sarakunan gargajiya a jihar da yiwa gwamnatinsa zagon kasa wajen kokarin kawo karshen matsalar tsaron jihar.

Gwamnan, a wata ganawa da yayi da shugabannin hukumomin tsaro a jihar ranar Alhamis, ya ce sarakunan gargajiya ba sa taka nasu rawan wajen yaki da yan bindiga.

Ya ce hakan ya sa matsalar tsaro ta kara tsanani a jihar kwanakin nan, Premium Times ta ruwaito.

Taron ya samu halartan Malaman addini, sarakunan gargajiya da yan jarida a gidan gwamnatin jihar dake Gusau.

Matawalle ya ce wasu sarakunan gargajiya na taimakawa kungiyoyin yan sakai a yankunansu duk da cewa gwamnati ta haramta, kuma hakan ya sa yan bindigan ke kai hari.

Bayan haka, gwamnan ya caccaki Mai marataba, Sarkin Anka, Attahiru Ahmad, kan jawabin da yayi cewa gwamnati ta amincewa mutane daukan makamai don kare kawunansu tun da gwamnati ta gaza waje kare al'umma.

Gwamnan yace "babu dadi a ce mutumin da ake ganin girmansa irin shugaban sarakunan gargajiyan jihar yayi hira da manema labarai yana kalubalantar kokarin da gwamnati da jami'an tsaro ke yi."

Matawalle ya ce hakkin tsaro na kowa ne ba na gwamnati kadai ba.

Ya ce idan mutan jihar da sarakuna basu son sulhun da gwamnatinsa da yan bindiga, sai janye hannunsa.

A bangare guda, wata kotu dake zaune a Ilori, birnin jihar Kwara, ya yankewa wani direba hukuncin shekaru biyu a gidan kaso kan amfani da kudin da ba nashi ba.

Direban, mai suna Adetunji Tunde Oluwasegun, ya yi amfani da kudi milyan biyu da wata mata Sherrifat Omolara Sanni ta tura asusun bakinsa na GTB cikin kuskure.

Ofishin hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da shi a kotun ranar Litinin, 18 ga Junairu, 2021.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN