Duba jerin muhimman aubuwan da suka faru a Najeriya a makon da ya gabata

Kamar yadda muka saba a kowanne mako, mun tattaro muku wasu daga cikin muhimman labaran da suka fi jan hankali a Najeriya a makon da muke bankwana da shi


.

Lahadi: Ƴan bindiga sun kashe mutum 7 da ƙona buhun masara 330 a Kaduna

Harin Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa ƴan bindiga sun kai hari a kasuwar Galadimawa da ke Ƙaramar Hukumar Giwa, lamarin da ya ja aka tafka mummunar asara.

A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya fitar, ya bayyana cewa 'yan bindigar sun kashe 'yan banga biyu da wasu mutum biyar.

A harin dai, 'yan bindigar waɗanda suka je kasuwar kan babura 15 sun yi sanadiyar ƙonewar wata ƙaramar mota da kuma buhunan masara 330 da ke cikin wata tirela mallakar wani direba mai suna Alhaji Yusuf Tumburku.Rahotanni dai sun ce ɓarayin tun farko sun shiga kasuwar ne da misalin ƙarfe huɗu na yamma inda suka buɗe wa ƴan bangar wuta.

Amma daga baya jami'an tsaro da suka haÉ—a da sojojin sama sun bi É“arayin inda suka samu nasarar kashe wasu daga cikinsu, kamar yadda sanarwar da kwamishinan ya fitar ta bayyana.

Short presentational grey line

Litinin: An bayar da belin matar da ake zargi da kashe 'ya'yanta a Kano

Kotu

An bayar da belin matar da ake zargi da kashe Æ´aÆ´anta biyu a Kano a kwanakin baya.

An bayar da belin nata ne kan dalilan rashin lafiya amma duk da hakan kotu ta ce za a rinƙa kai ta asibitin masu taɓin hankali domin duba lafiyarta da sanar da kotu halin da take ciki.

Lamarin wanda ya faru tun a watan Oktoba a Unguwar Sagagi Layin 'Yan Rariya a birnin Kano, da farko an bayyana cewa saɓani ne da mijinta saboda ya yi mata kishiya a watannin baya ya kai ga kisan ƴaƴansu.

Amma daga baya mahaifiyar matar da mijinta sun ce ta daÉ—e tana fama da rashin lafiya mai nasaba da iskokai kuma tana nuna alamun hakan.

Ta kuma shaida cewa tun da ta aurar da Æ´arta shekara shida da suka gabata, Æ´arta take tafka rikici da mijinta. "Kullum faÉ—a suke da mijinta," in ji uwar matar.

A halin yanzu dai lauyoyin matar da ake zargin ne suka nemi belinta, kuma tana asibitin Aminu Kano a ɓangaren duba lafiyar ƙwaƙalwa.

Haka kuma za ta ci gaba da bayyana a gaban kotun majistare da ke Gidan Murtala.

Short presentational grey line

Talata: Burtaniya ta nesanta kanta daga zargin Yakubu Gowon da wawushe Baitul-malin Najeriya

Yakubu Gowon

Kasar Burtaniya ta nesanta kanta daga zargin wawushe baitul-malin Najeriya da wani É—an majalisar ta, Tom Tugendhat ya yiwa tsohon Shugaban Najeriyar Yakubu Gowon.

Matakin ya biyo bayan koken da wata ƙungiya, Igbo for a Progressive Nigeria (IPAN) ta gabatar ga majalisar dokokin Burtaniyan, suna neman cikakken bayani game da zargin.

A yayin wata muhawara a É—akin taro na Westminster a ranar 23 ga watan Nuwamba ne dai Tugendhat ya zargi Gowon da wawure rabin kuÉ—aÉ—en da aka tara a Babban Bankin Najeriya yayin da yake kan mulki.

Jaridar The Nations ta rawaito wata jami'a a ofishin kula da ƙasashe renon Burtaniya Angela, ta bayyana cewa Tom Tugendhat ya yi wannan kalami ne a kashin kansa, ba da yawun Burtaniya ba.

Short presentational grey line

Laraba: An kama 'yan ƙungiyar asiri 15 a Jihar Legas

'Yan sandan Legas

Rundunar 'yan sandan Legas ta faɗa jiya Talata cewa ta kama aƙalla mutum 15 bisa zargin aikata laifuka a ƙungiyoyin asiri da kuma ta'addanci a jihar.

Kazalika, ta ce ta ƙwato miyagun makamai daga hannun gungun mutanen da ke addabar mazauna yankunan Lekki da Ajah.

Kakakin rundunar Muyiwa Adejobi ya ce an kama waÉ—anda ake zargin ne kafin su samu damar aikata laifukan da suka tsara.

Ya ce jami'ansu sun kama wani matashi mai shekara 20 mai suna Taiye Lasisi ranar Litinin ɗauke da bindiga ƙirar gida bayan an nemi agajinsu a yankin Ikorodu.

Bayan kama shi ne kuma aka tsananta bincike, inda aka kama wasu mutum 13 'yan ƙungiyar asiri ta Aiye Confraternity, a cewar Mista Adejobi.

Ya ƙara da cewa sun sake kama wani ɗan ƙungiyar asirin mai suna Lekan Razak mai shekara 20 yayin da yake yunƙurin aikata fashi a kan Titin Ibomide da ke Lekki a Litinin ɗin da misalin ƙarfe 4:00 na dare.

Short presentational grey line

Alhamis: Wani mutum ya cinna wa kansa wuta a jihar Filato

Ƴan sandan Najeriya

Wani mutum da ake zargin ya cinna wa kansa wuta ya mutu, jim kaÉ—an bayan an garzaya da shi asibiti.

Lamarin dai ya afku ne a birnin Jos na jihar Filato inda wasu shaidu suka ce mutumin mai suna Muhammad Ibrahim mai kimanin fiye da shekaru talatin ya cinna wa kansa wuta ne bayan wata rashin jituwa da ya samu tsakaninsa da mahaifinsa da Æ´an uwansa.

Wani Malam Hassan Umar wanda yake sana'a a kusa da wurin da lamarin ya faru a Unguwar Zaria Crescent cikin wani lambu a birnin Jos, ya shaida wa BBC cewa sun hangi Muhammad Ibrahim wanda magidanci ne da Æ´aÆ´a biyu yana shan wani abu a galan.

A cewarsa, daga baya sai suka ga wuta ta kama sai suka nemi ruwa ba su samu ba, suka samu ruwan leda shi ma ya ƙi kashe wutar, sai dai a kwata suka yi amfani da shi suka kashe wutar, ko da suka kashe wutar ta riga ta ƙona shi.

BBC ta tuntuɓi mai magana da yawun 'yan sanda na Filato ASP Ubah Gabriel, domin jin ƙarin bayani kan lamarin, sai dai ya aiko mana da rubutaccen saƙo cewa har yanzu suna kan tattara bayanai don haka zai nemi mu.

Short presentational grey line

Juma'a: Allah Ya yi wa Iyan Zazzau Bashir Aminu rasuwa

Iyan Zazzau

Iyalansa ne suka tabbatar wa da BBC labarin mutuwar tasa, inda suka ce ya rasu ne a Legas bayan gajeruwar rashin lafiya.

Iyan Zazzau na daga cikin waÉ—anda suka nemi sarautar Sarkin Zazzau bayan rasuwar Marigayi Sarki Shehu Idris a watan Satumban 2020.

Marigayin dama yana da ciwon suga kamar yadda iyalansa suka tabbatar.

Kafin rasuwarsa, dama wata kotu a Kaduna tana sauraren ƙarar da ya shigar inda yake ƙalubalantar naɗin da aka yi wa sabon sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli.

Iyan Zazzau Bashir Aminu ya fito ne daga gidan Katsinawa É—an tsohon Sarkin Zazzau na 17 Malam Muhammadu Aminu.

Iyan Zazzau ya taɓa rike sarautar Dan Madamin Zazzau kafin ya zama Hakimin Sabon Gari.

Kuma yana daga cikin waɗanda aka rinƙa hasashen cewa zai zama Sarkin Zazzau a kwanakin baya.

Short presentational grey line

Asabar: EFCC ta kama mutum 21 da zargin zamba ta intanet

Masu zamba a Internet

Jami'an hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya reshen Jihar Legas sun kama mutum 21 bisa zargin aikata zamba ta intanet.

EFCC ta ce ta kama mutanen ne na wata ƙungiyar aikata laifuka ta intanet yayin wani samame da asubahin ranar Laraba bayan ta samu wasu bayanan sirri game da ayyukan nasu.

Bayan kama sun ne kuma, hukumar ta ƙwace ababen hawa guda 12 da suke amfani da su da kwamfutar laptop da kuma wayoyin hannu.

Hukumar ta bayyana sunayen mutanen kamar haka: Shittu Yakubu, Akinsola Afeez, Adeniyi Joseph, Opeyemi Wahab, Idris Sunday, Lawal Moshood, Jubril Yusuf, Olusegun Mohammed, Adekunle Adesanya, and Damilola Abijide.

Sauran su ne Sola Adio, Oladipo Ademola, Damilola Adewale, Akinsola Ridwan, Ogunlaye Damilare, Falaye Peters, Magnus Toni, Onanuga Ahmed, Bolarinwa Segun, Onanuga Olawale, and Ayomide Afeez.

EFCC ta ce za ta gurfanar da su a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

Source: BBCHausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN