Boko Haram ta aikata wani mugun aiki a jamhuriyar Nijar, duba abinda ya faru

A ƙalla sama da fararan hula 70 ne aka kashe a wasu tagwayen hare-hare da ake zargin yan kungiyar Boko Haram ne suka kai kan wasu ƙauyuka biyu dake ƙasar Nijar kusa da iyaka da kasar Mali.

Kimanin mutum 50 ne aka kashe a ƙauyen Tchombangou sannan 17 suka ji mummunan rauni kamar yadda wani jami'in tsaro ya tabbarwa Reuters ya kuma nemi da a sakaye sunansa, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Wata majiya daga wani jami'in harkokin cikin gida na ƙasar ta Nijar da shima ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da an kashe sama da kimanin mutum 30 a Zaroumdareye.


Da jin faruwar wannan kazamin al'amari ne, gidan jarida na Reuters ya yi kokarin jin ta bakin manyan jami'an da alhakin hakan ya shafa na ƙasar amma haƙansu ba ta vimma ruwa ba.

fama da da hare-haren taaddanci daga dakarun kungiyoyi da suke da alaƙa da kungiyar alQaeda. Daga iyakokin yamma, hare-haren kuma ya fi kamari a yankunan Mali, Burkina Faso, sai kuma kudu maso gabas inda hare-haren ya kazanta a yankunan Nijar da Najeriya.

Legit.ng ta rawaito cewa rundunar sojin Najeriya ta bayyana salon da ta bi na ceto yaran makarantar sakandire ta kimiyya dake ƙanƙara su 344 waɗanda yan ta'adda suka sace ranar 11 ga Disamba, 2020.

Kazalika, ta mayar da martanai ga ikirarin shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, akan cewa kungiyarsa ce keda alhakin sace daliban.

A cewar rundunar Sojin, ta yi amfani da salo wajen kubutar da yaran don tabbatar da cewa babu wani yaro da aka kashe ko ya ji rauni a hannun 'yan ta'addar, kamar yadda Punch ta rawaito

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN