An dauke wani jigon Miyetti Allah a garin Kanya jihar Kebbi


An dauke wani jigo na kungiyar Makiyaya na Miyetti Allah na reshen karamar hukumar Danko-Wasagu da ke Masarautar Zuru a kudancin jihar Kebbi Mai suna Alhaji Mande Kanya.

Rahotanni sun ce wasu mutane dauke da makamai, da ake zargin Yan sa Kai ne, sun dira garin Kanya da ke karkashin karamar hukumar Danko-Wasagu da misalin karfe 5:15 na yammacin ranar Lahadi suka yi awon gaba da Alhaji Mande Kanya wanda gurgu ne, domin da sandan guragu yake tafiya.

Rade radi da ke yawatawa a garin Kanya sun yi zargin cewa mutanen sun kwabe sandunan guragu da Mande Kanya ke amfani da su, kuma suka dora shi a kan babur suka yi awon gaba da shi.


Sai dai har lokacin rubuta wannan rahotu, rundunar Yan sandan jihar Kebbi bata fitar da bayani ba kan lamarin ba.

Amma mun samo daga majiya mai tushe cewa masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro a jihar Kebbi, sun dauki matakin ganin cewa an shawo kan lamarin bisa tsarin doka da oda.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN