Hotunan hatsarin jiragen sama da dalilai da ke haddasa aukuwan hatsarin jirgin sama


Sau da dama mutane kan yi mamaki idan suka ji cewa an yi hatsarin jirgin sama. Sai dai sukan manta cewa akwai ababe da dama da ke iya haddasa hadarin jirgin sama ko a sararin samaniya ko a kasa.


Wasu daga cikin dalilai da ke haddasa hatsarin jirgin sama sun hada da rashin tsara manhajar aikatau na jirgi da ake kira Flight Management Computer FMC, wanda ke dauke da tsaruka da dama ciki har da lissafin gudun injin jirgi, adadin mai da jirgi zai zuka da sauran nau'in aikatau.


Kazalika, wani dalili da ke haddasa hatsarin jirgin sama ya hada da samun matsalar injin jirgi yayin da jirgi ke tafiya a sararin samaniya, ko lokacin da jirgi ke kokarin tashi ko sauka.


Sai kuma dalilin matsalar rashin kyaun yanayi, wanda ke shafan yadda matuki ke sarrafa jirgin sama da nau'in aikatau na jirgi wanda ke cin karo da yanayi maras kyau, sakamakon haka akan iya samun aukuwan hatsarin.


Wadannan kadan kenan daga cikin dalilai da ke iya haddasa hatsarin jirgin sama.
Latsa nan ka shiga group din mu don samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN