Yanzu-yanzu: Gwamna Matawalle ya kulle makarantun Zamfara dake makwabtaka da Katsina da Kaduna


Labarin dake shigowa da duminsa na nuna cewa gwamnatin jihar Zamfara ta bada umurnin kulle dukkan makarantun jihar dake makwabtaka da jihohin Katsina da Kaduna.

TVC ta ruwaito cewa gwamnatin ta tabbatarwa iyayen daliban makarantun dake cikin Gusau da ba'a kulle ba cewa kada su damu akwai isasshen tsaro a cikin gari.

Kwamishanan ilmin jihar Zamfara, Ibrahim Abdullahi, ya bayyana cewa ma'aikatarsa ta baiwa gwamnan shawaran rufe wadannan makarantu gudun kada a faru da jihasr Katsina ya afka musu.

Yace: "A nan jihar Zamfara muna kokarin kiyaye faruwan abinda ya faru a Kankara."

"Saboda haka mun baiwa gwamna shawara ya rufe wasu makarantun kwana dake iyaka da jihar Kaduna da jihar Katsina."

"Ba dukkan makarantun kwana dake Zamfara aka rufe ba."

Ga jerin makarantun da gwamnatin jihar ta rufe:

GASS Zurmi

GSS Birnin Magaji

GSSS Bayumkafi

GSS Ape

GSSS Bokuyum

GSSS Dan Sadau

GDSS Nasarawa Malayi

GDSS Gusami

GDSS Gudun Kore

Mun kawo muku cewa kungiyar Boko Haram ta sanar da cewa ita ce keda alhakin sace dalibai fiye da 300 daga makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara a jihar Katsina, kamar yadda HumAngle ta rawaito.

A cewar HumAngle, shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya ce har yanzu basu tuntubi kowa dangane da wasu sharuda na sakin daliban ba.

Jaridar ta ce, Shekau ya sanar da hakan ne a cikin wani sakon sautin murya mai tsawon mintuna 4:28 da ya fitar da duku-dukun safiyar ranar Talata.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN