Yan ta'adda sun yi awon gaba da Ango da abokinsa bayan daurin aure


Yan ta'addan sun yi awon gaba da ma'aikatan tallafi biyu a jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya yayinda suke hanyar dawowa daga daurin aure, majiya daga jami'an tsaro sun bayyana ranar Asabar.

Mutanen da aka sace sun ma'aikacin kungiyar ciyar da al'umma na majalisar dinkin duniya WFP, wanda shine Angon da kuma abokinsa na kungiyar RedCross da ya raka shi.

Majiyoyin sun bayyana cewa yan ta'addan ISWAP ne suka sace su ranar Laraba, kusa da kauyen jakana.

"Yan ta'addan ISWAP sun dauke ma'aikatan tallafi biyu yayinda suka tare hanya kusa da Jakana," wata majiyar UN ta bayyana AFP.

Matasan na hanyar komawa Maiduguri daga jihar Adamawa yayinda aka taresu misalin karfe 1:30 na rana, majiyar ta kara.

Ma'aikacin WFP "ya yi daurin aurensa ranar 28 ga Nuwamba kuma abokin aikinsa na Red Cross ne babban abokin ango," cewar majiya daga majalisar dinkin duniya.

Wata majiya a gidan Soja ta tabbatar da aukuwan lamarin.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN