Allah kaɗai zai iya tsare iyakokin Nigeria da Nijar, in ji Buhari


Shugaba Muhammadu Buhari ya ce duba da girman iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar, Allah ne kadai zai iya tsare iyakokin yadda ya kamata, Daily Nigerian ta ruwaito.

Da ya ke jawabi yayin karbar bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, wadda ke jagorancin tawagar sa ido kan zabe ta ECOWAS a Nijar, Buhari ya ce zai iya duk mai yiwuwa don kawo zaman lafiya a yankin na Sahel.

Allah kadai zai iya tsare iyakokin Nigeria da Nijar, Buhari. Hoto: @BashirAhmaad

A cewar sanarwar da Femi Adesina, mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan labarai, shugaban kasar ya jinjinawa takwararsa na Nijar, Shugaba Muhamadou Issoufou, "don bai yi yunkurin sauya kundin tsarin mulki ba don zarcewa bayan kure wa'adinsa biyu."

Adesina ya ce ya jiyo Buhari ya cewa, "Daga Daura na fito, kilomita kadan ke tsakanin mu da Jamhuriyar Nijar, don haka na dan san wani abu game da kasar. Shugaban kasarsu mai mutunci ne kuma mu kan tuntubi juna sosai. Ba zai wuce tsawon lokacin da kudin tsarin mulki ta diba wa shugabanni ba a kasarsa.

"Kazalika, muna da iyaka mai tsawon kilomita 1,400 wadda Allah ne kadai zai iya kiyaye ta yadda ya dace. Zan yi magana da shugaban kasar in bawa kasarsa gudunmawar mu. Ya zama dole muyi duk abinda zamu iya don kawo tsaro a yankin Sahel don duk zai amfane mu."

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya taya Shugaba Buhari murnar ceto yaran makarantar Kankara da murnar cika shekaru 78 a duniya a makon da ta gabata.

Ya yi alkawarin ECOWAS zata tabbatar anyi zaben adalci cikin zaman lafiya a Jamhuriyar Nijar duk da matsalolin da ake fama da su a kasar, ya kara da cewa ya fara tuntubar masu ruwa da tsaki a harkar.

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Source: Legitimate


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN