Paris Club: Shugaba Buhari ya bamu Naira Biliyan 47 inji Gwamnan Jigawa


Mai girma gwamnan Jigawa ya bayyana cewa jiharsa ta karbi wasu kudinta da ta ke jira daga hannun gwamnatin tarayyar Najeriya.

The Nation ta rahoto cewa Muhammadu Badaru Abubakar ya tabbatar da karbar fiye da Naira biliyan 47 daga hannun gwamnatin tarayya.

Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar yace an dawo masu da wannan kudi ne saboda abin da gwamnatin jiha ta kashe wajen gina filin jirgi.

Bayan haka akwai kudin bashin Paris Club wanda gwamnati ta karba da yanzu ya dawo hannun gwamnatin jihar Jigawa, jaridar ta rahoto haka.

Gwamnan ya yi wannan bayani ne a ranar Lahadi, 6 ga watan Nuwamba, 2020, wajen kaddamar da titin Balago zuwa Auno mai-cin kilomita 42.

Badaru Abubakar ya ce an ba jiharsa Naira biliyan 37 na bashin Paris Club da gwamnatin tarayya ta karba.

Bayan haka gwamnatin tarayya ta aiko wa jihar Naira biliyan 10 a matsayin abin da ta batar wajen gina filin jirgin sama na jihar Jigawa a Dutse.

Da yake na shi jawabin, shugaban gwamnonin APC, Atiku Bagudu, ya yabi gwamnan Jigawa.


Badaru Abubakar Hoto: www.pmnewsnigeria.com

Sanata Atiku Bagudu ya ce Badaru Abubakar ya ciri tuta wajen takatsan-tsan a kashe dukiyar al’umma.

Atiku Bagudu yake cewa titin da za a gina daga Balago zuwa Auno zai taimaka wa tattalin arzikin mutanen wannan yanki da sauna al’ummar yankin.

A baya kun ji yadda Boko Haram su ka yanka wani Bawan Allah wanda Matar shi ta haihu, ya je neman masu abinci a lokacin da aka kai hari a Zambari.

Bayan kwana 7 da harin Zabarmari, Mai Garin kauyen. ya fito ya bada labarin abubuwan da suka auku a lokacin da aka kawo masu hari a wata Asabar.

Sannan Mai Garin Zabarmari yace karya ne, ba su bukatar amincewar Sojoji kafin su shiga gonakinsu.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN