Rundunar NSCDC na jihar Nassarawa ta kama wani mutum dan shekara 46 mai suna Amos John Ewuga bisa zargin yin sojan gona kasancewa mai mukamin Major a sojin Najeriya.
An kama Amos wanda dan asalin karamar hukumar Nassarawa Eggon ne bayan koke da jama'a da dama suka shigar wajen NSCDC kan zargin cewa Amos yana karban kudaden jama'a da karyar cewa zai sama masu aikin soji, dan sanda, sojin ruwa ko na sama.
Lamari da aka yi zargin ya karbi miliyoyin Naira daga hannun bayin Allah ta hanyar yaudaran cewa zai sama mau aiki.
Kakakin hukumar NSCDC na jihar Nassarawa Muhammad Suraj Idris, ya ce an kama Amos ne ranar Juma'a a kan hanyar Akwanga-Keffi-Abuja.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari