Mahaifiyar yara biyar ta rataye kanta har ta mutu saboda talauci da kuncin rayuwa


Wata mata uwar yara biyar mai suna Ifeoma Otubo mai shekara 45 ta mutu bayan ta rataye kanta a icen mangoro har ta mutu a karamar hukumar Ezza ta arewa a jihar Ebonyi.

Mahaifiyar yara biyar, Ifeoma ta kashe kanta ne a bayan gidanta da sanyin safiyar Lahadi 20 ga watan Disamba.


Mun samo cewa Ifeoma ta yi kokarin kashe kanta a 2014 amma aka ceto ta. Bayanai sun ce ta yi haka ne saboda tsananin talauci da kuncin rayuwa.

Dan uwanta mai suna Christopher Oyigbo, ya ce kafin ta kashe Kanta, Ifeoma ta sha kokowa game da matsanancin talauci, damuwa da kuncin rayuwa tare da gazawa wajen daukan dawainiyar yayanta biyar.

Ya Kara da cewa ci gaba da rikicin kabilanci tsakanin alumman Ezza da Eziulo a karamar hukumar Ishielu ya taimaka wajen jefa Ifeoma cikin talauci.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN