Magidanci ya banka wa kanshi wuta har ya mutu saboda tsananin talauci da kuncin rayuwa


Daga jihar Benue, mun samo rahotun yadda wani ma'aikacin karamar hukumar Gwer ta gabas mai suna Aondona Yaga ya banka wa kanshi wuta ya kone har lahira a garin Aliade.

Majiyarmu ta ce Kakar Yaga ta ce ya yi fama da matsanancin kuncin rayuwa tsawon shekara uku da suka gabata. Ta ce Yaga ba cikakken ma'aikacin karamar hukuma bane, kuma ba a biya shi alawus da yake karba ba tsawon shekara uku.


Ta kara  da cewa " Sakamakon haka lamurra suka yi tsauri ga Yaga, ana cikin wannan kuncin rayuwar ne sai ya kamu da rashin lafiya. Ta ce baya da kudin sayen abinci balle magani. Daga bisani dai Yaga ya kashe kanshi, kuma jama'an gari suka yi watsi da gawarsa, babu wanda ya damu da ita sai ita tsohuwa wanda Kakarshi ce.Jami'in kula da watsa labarai na karamar hukumar Gwer ta gabas mai suna Mr.Chris Ayi, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma shaida cewa Yaga ma'aikacin wucin gadi ne a karamar hukumar, sai dai bai yi wani karin bayani ba.


Har zuwa lokacin rubuta wannan rahotu, babu wanda ya kai dauki wajen gawar Yaga,  sai Kakarshi ce kadai a tare da gawar wacce ke gaban gidansa.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN