Hotunan yadda soji suka aika gagararrun yan bindiga 2 barzahu, suka dagargaza sansaninsu


Dakarun soji  da ke gudanar da aikin  WHIRL STROKE Bataliya ta 177 da sanyin safiyar ranar 9 ga watan Disamba, sun kai farmaki zuwa mabuyar yan bindiga da ke Angwan Mada kusa da Tunga a karamar hukumar Nassarawa ta jihar Nassarawa a tarayyar Najeriya.

Bisa amfani da bayanan sirri, soji sun farmaki manyan yan bindiga biyu kuma suka kwace bindigogi guda 20 kirar gida bayan sun kashe yan bindigan.


Kazalika jami'an soji sun kama albarussai da dama da sauran haramtattun makamai.

Daga bisani soji sun dagargaza sansanin yan bindigan, kuma suka bi sauran yan bindiga da suka tsere domin kamasu kuma su halaka su.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN