Fusatattun matasa sun banka wa saurayi wuta har ua kone bayan an yi zargin cewa ya yi kokarin kwace wayar salula a hannun wata mata a birnin Uyo babban birnin jihar Akwa-Ibom .
ISYAKU.COM ya samo cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 na safe ranar Laraba 17 ga watan Disamba a kan hanayar Abak ka ke birnin Uyo.
Wani ganau ya shaida wa manema labarai cewa wanda aka akashe, yana daya daga cikin bata gari da suka dade sun addaban jama'a a wannan unguwa da ke birnin Uyo, musamman a "Ibom-Plaza" wajen hhada-hadar kasuwanci.
Bayan kone gawarsa, matasa sun baje gawarv a wurare masu daukan ido a kan titi domin ya zama izna ga sauran bata gari.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari