Rahotanni daga unguwar Jakande da ke Lekki a birnin Lagos sun ce wani dereban mota ya kwada wa ma'aikacin LATSMA tabarya a kai bayan zafafan cacan baki lokacin da jami'ai suka tsayar da shi domin bincike.
Direban mai suna Fred Onwuche ya kwada wa jami'in LASTMA Mr. Kosoko Razak tabarya a kai bayan an tsayar da motarsa domin yana tuki ba tare da amfani da belt na kujerar mota ba.
An kama direban motar, yayin da aka garzaya asibiti da Mr. Kosoko domin samun kulawan Likita sakamakon raunuka da direban Fred ya yi masa.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari