Wata yarinya ta banka wuta a gidan da saurayinta mai suna Jude yake ciki tare da mahaifiyarsa da yaro mai shekara biyu da karfe 1:30 na dare a Gboko ta kudu a jihar Benue ranar 7 ga watan Disamba.
Saurayinta ya ce ya fasa aurenta saboda halayenta na rashin ragowa gareshi da mahaifiyarsa. Bisa wannan dalili ne yarinyar ta dauki wannan mataki kasancewa ya ce ta kwashe kayanta ta fice ta bar masa gidansa.
Rahotanni sun ce da dare, sai yarinyar ta dawo tare da wasu mutum uku a kan babur, suka yage net na sauro da ke tagar dakin, sai suka zuba wani abu da ake zargin cewa fetur ne, daga bisani sai yarinyar ta kyasta ashana ta jefa ta taga, nan take wuta ta kama yayin da saurayinta Jude tare da mahaifiyarsa da yaro mai shekar uku suka kama da wuta.
Rahotun ya kara da cewa daga bisani yarinyar ta hau babur da suka zo da shi suka yi tafiyarsu. Ihu da Jude ya yi ta yi ya ankarar da jama'a da suka zo suka balle kofar daki, kasancewa an gano yarinyar ta kulle kofar da makulli daga waje kafin ta kyasata ashana ta jefa a dakin.
An ceto Jude, mahaifiyarsa da yaro da kuna a jikinsu. Sai dai kuna da ke jikin Jude ta fi tsananta, kuma an garzaya zuwa Asibiti da shi domin samun kulawan Likitoci.
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari