Allah ka tsine ma wadanda suka kashe Kanawa 16 a kan hanyar Abuja zuwa Kano>>Ganduje


Gwamna Abdullahi Ganduje ya roki Allah ya tsine wa yan bindiga da suka kashe mutum 16 yan asalin jihar Kano da ke kan hanyar dawowa daga Abuja zuwa Kano.

A wata sanarwa da wani Hadimin Ganduje mai suna Abba Anwar ya fitar kan lamarin, Ganduje ya ce " Mun kadu da samun labarin kisan mutum 16 yan asalin garin Danbatta da suka rasu sakamakon farmaki da yan bindiga suka kai masu a babban hanyar mota daga Abuja zuwa Kano.

Wannan labari na  da ban takaici.  Mun tausaya tare da yin ta'aziyya ga iyalan wadanda yan bindiga suka kashe da kuma jama'an karamar hukumar Danbatta, da jama'an jihar Kano.

Allah ka yafe wa mamatan zunubansu. Allah ka tsine wa wadanda suka aikata wannan aiki. Ba abin da ya fi wannan takaici.

Amadadin al'umman jihar Kano gaba daya, ina mika ta'aziyya ga iyalan mamatan dal'umman Danbatta, Allah ka yafe masu kurakuransu" inji Gwamna Ganduje.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN