Yawaitar bacewar mazakuta: Matasa sun yi zanga zangar lumana a garin Daudu - Hotuna


Matasa a garin Daudu da ke karamar hukumar Goma a jihar Benue, sun gudanar da zanga zangar lumana ranar Lahadi 1 ga watan Satumba bisa zargin karuwar bacewar Mazakutar maza a garin.

Matasan sun yi zargin cewa mutum 7 ne suka rasa Mazakutarsu a wani yanayi mai ban mamaki a garin.

Zanga zangar ta faro ne daga Kasuwar Daudu har zuwa babban hanyar mota ta Makurdi zuwa Lafia, yanayi da ya haifar da cinkoson ababen hawa da dama a hanyar kafin yansanda suka  je suka tarwatsa matasan.


Kazalika rahotu ya ce wani matashi ya kashe kansa ranar 11 ga watan Oktoba bayan an zarge shi da sace Mazakutar wani matashi a garin.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN