• Labaran yau

  Yan ISIS sun kashe mutum 50 suka yi gunduwa-gunduwa da gawakinsu


  Yan kungiyar ISIS sun fille kan mutum 50 kuma suka yi gunduwa gunduwa da sassan jikinsu a Arewacin Mozambique.

  Yan kungiyar sun gudanar da wannan danyen aiki ne a cikin wani filin wasan kwallon kafa. Sun daure hannayen kauyawa wadanda suka kama daga gundumar Cabo Delgado sa'annan suka sassare su.

  BBC ta ruwaito cewa yan bindigan sun kama mata da yara da dama a kauyen Nanjaba, yayin da suka kashe fiye da mutum 50 a harin da suka kai a garin Muatide.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yan ISIS sun kashe mutum 50 suka yi gunduwa-gunduwa da gawakinsu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama