Yadda wata babban mota ta haddasa hatsari da dama a lokaci daya garin neman gudu bayan laifi


Jama'a da dama sun sami raunuka sakamakon wani hatsari da wata babban motar daukan kaya ta haddasa a tagwayen hanyar mota da ke Ikot kusa da hanyar BCA a Umuahia na jihar Abia.

ABN TV ta labarta cewa wata babban mota ce ta yi kokarin canja hannu, sakamakon haka ta buge wani Keke Napep dauke da wata mata da diyarta kuma suka sami raunuka.


Bayan da ya tsaya domin ya duba matsalar, sai direban motar ya sake jan motarsa ya nemi ya gudu, amma wata mota Corolla ta tare shi. Direban babban motar ya buge motar Corolla garin neman ya gudu.


Kazalika babban motar ta buge wani karin Keke Napep garin neman gudu. Sakamakon haka ya haddasa hadurra da dama a lokaci daya. Direban motar ya yi tsalle daga cikin motar ya tsare, bayan ya ga fusatattun matasa sun nufo shi.

Sai dai yaron mota bai tsira ba, kuma matasa sun kama shi suka mika shi ga yansanda har sai direban motar ya je wajen yansanda domin bincike.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN