Fusatattun matasa sun kone wata babban motan daukan kaya bayan ta murkushe wani mai tura amalanke ya mutu nan take a birnin Onitsha ranar Talata.
Igbere TV ta labarta cewa lamarin ya faru ne da karfe 9: 55 na safe ranar Talata 10 ga watan Nuwamba. a Uweka ta sama a kan hanyar Onitsha zuwa Owerri.
Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne sakamakon matsanancin gudu da direban motar yake yi.
Daga bisani sai motar ta kwace daga hannunta ta bi ta kan mai tura amalanke kuma ta murkushe shi har lahira nan take.
Sakamakon haka direban motar ya gudu cikin jama'a, matasa cikin fushi suka kone motar.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI