Tsohon Janar ya maka hukumar soji Kotu sakamakon yi masa ritayan dole


Janar Abubakar Sa'ad mai murabus ya maka hukumar sojin Najeriya gaban Kotun ma'aikata a Abuja yana kalubalantar ritaya da aka yi masadaga aikin soji.

Wadanda aka yi kara sun hada da babban Kwamandan sojin Najeriya CDS, Ministan tsaro da kuma Ma'aikatan juka da ayyukan soji.

Sa'ad na neman Kotun ta haramta ritaya da aka yi masa daga soji ranar  9 ga watan Yuni, 201, kuma ta tabbatar cewa haka ya saba wa dokokin ayyukan sojin Najeriya da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, da kuma dokar soji  Armed Forces Act Cap A20 LFN 2004. Da kuma kundin dokokin soji na 2015.

Sa'ad ya ce  an dauke shi aikin soji a kwas na 35 na kananan hafsoshin soji na 1986, kuma aka yi masa ritayan dole ranar 9 ga Satan Yuni 2016 yana da shekara 32 a aikin soji marmakin shekara 35 ko shekara 60 da hauhuwa da doka ta tanada. 


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN