Bayan shekara biyar, mutumin da ya yi tattaki da kafa daga Gombe zuwa Abuja domin murnar nassarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2015, Mr Dahiru Euba, ya sami kayautar mota da Naira Miliyan biyu daga Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe.
Gidan talabijin na Channels ta labarata cewa ana zargin Dahiru ya kamu da ciwon kafa bayan tattakin sakamakon doguwar tafiya da ya yi da kafa domin taya Buhari murna sakamakon nasara daya samu a zaben mulkinsa na farko.
Mai shekara 50 a Duniya, Dahiru direban mota ne dan asalin karamar hukumar Dukku a jihar Gombe, ya kasance cikin matukar farin ciki bayan Gwamna Inuwa ya ba shi kyautar motar da Naira Miliyan 2.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari