• Labaran yau


  Sa man goge baki wai domin tsukewar farji yana haddasa matsaloli ga mace>>Kwararren Likita


  Dr Olufunmilayo Likita ne da ya yi gargadi ga mata cewa su daina sa  man goge baki a cikin al'aurarsu wai domin haka zai sa al'aurarsu ya tsuke.

  Likita Olufunmilayo ya ce yin haka yana da matukar hadari ga lafiyar farjin mace. Ya ce man goge hakori yana da radadi ga farjin wasu mata, kazalika yana iya haddasa matsaloli da dama.

  Ya ce sakamakon amfani da man goge hakori a farjin mace, za ta iya kamuwa da cutuka da ke iya haddasa matsanancin warin farji, fitowar ruwa masu kazanta daga farji ba da wani dalili ba da kuma yiwuwar kamuwa da cutar mahaifa da zai iya kaiwa ga matsalar rashin samun juna biyu balle haihuwa.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Sa man goge baki wai domin tsukewar farji yana haddasa matsaloli ga mace>>Kwararren Likita Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama