Nan take soji sun aika wasu yan fashi da makami lahira da gaggawa, duba dalili


Wasu yan fashi da makami guda hudu sun bakunci lahira bayan sun yi musanyar wutan bindigogi tsakaninsu da sojin  Operatives of Operation Delta Safe, OPDS.

Rahotanni sun ce wadannan yan fashi da makami sun dade suna addabar al'umman Oyiore da ke karamar hukumar Ethiope ta gabas a jihar Delta.


Yan fashin dai sun buda wa sojin wuta da bindigogi ne bayan sun gansu, lamari da ya sa sojin suka mayar da martani da ya kai ga bindige yan fashin har lahira nan take.


Kwamandan sashe na 1 OPDS na sojin Najeriya  Colonel Ahmed Sanni, Effurun, ya ce soji sun sami kiran ceton gaggawa daga al'umman Oyiore da karfe 10:04 na safe ranar 20 ga watan Nuwamba cewa yan fashi suna cikin garin.


Ya ce isar sojin ke da wuya sai yan fashi suka fara harbin soji da bindigoginsu. Ya ce soji sun mayar da martani sakamakon haka suka aika yan fashin lahira.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN