Na kaɗu matuƙa a yanka Manoma 43 da Boko Haram ta yi a Borno— Buhari


Boko Haram ta yi wa aƙalla manoma 43 yankan rago a jihar Borno.

Rahotanni sun ce manoman suna kan hanyarsu ne ta zuwa girbi a gonakinsu.

Wannan kisan gilla ya zo ne kwana ɗaya bayan jihar ta gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi.

‘Yan ta’addar na Boko Haram sun kuma yi garkuwa da mutane da dama, suka kuma raunata wasu da dama da harbin bindiga.

An kai wannan hari ne a ƙauyen Koshobe dake ƙaramar hukumar Jere ta jihar.

Rahotanni sun ce ‘yan Boko Haram ɗin sun kwantar da manoman ne, suka yi garkuwa da aƙalla 60 daga cikinsu.

Bayan nan ne suka ɗaure su, suka yi wa aƙalla 43 yankan rago.

Tuni an kai gawarwakin waɗanda aka kashe ɗin zuwa wani ƙauye, Zabarmari da yake kusa, in da za a binne su yau Lahadi.

An ce gonar da mafiya yawan waɗanda aka kashe suka yi aiki tana Zabarmari, kuma an ce mafiya yawansu sun zo Borno ne daga jihar Sakkwato.

Da yake mayar da martani ga wannan kisan gilla, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana kaɗuwrsa.

A wata sanarwa da Mataimakinsa Na Musamman A Kan Kafafen Watsa Labarai, Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya bayyana kisan a matsayin rashin hankali kuma abin Allah-wadai.

“Na yi Allah-wadai da kisan zaƙaƙuran manomanmu da ‘yan ta’adda suka yi a jihar Borno.

“Najeriya gaba ɗaya ta cutu da waɗannan kashe-kashe.

“Tunanina yana tare da iyalansu a wannan lokaci na baƙin ciki.

“Allah Ya ji ƙan su”, in ji Shugaba Buhari.

Source: labarai24


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN