• Labaran yau

  Kotu ta daure kasurgumin mai fyade rai da rai sau 7 da shekara 300 a Kurkuku


  Wata babban Kotun Bisho da ke gabacin kasar Afrika ta kudu ta daure wani kasurgumin mai fyade dan shekara 44 a Duniya Malibongwe Ncokolo rai da rai har sau 7, da shekara 300 a Kurkuku bayan ta kama shi da laifin yi wa mata da yan mata fyade.

  Ranar Juma'a 6 ga watan Nuwamba Kotun ta daure Ncokolo wanda kamunsa ranar 7 ga watan Yuni 2017 ya jawo fallasa da kawo karshen mumunan tashin hankali da mata da yan mata ke fuskanta na fyade a Mdantsane a Afrika ta kudu.

  Ncokolo ya yi ta cin zarafin mata da yan mata da keta, ta hanyar fyade da gayya tun 2014 kafin dubunsa ta cika a 2017  lokacin da ya yi kokarin yi wa wata yarinya fyade amma ta kubuta kuma ta nemi taimakon jama'a.

  Shaidu 140 ne tare da mata 22 da ya ci zarafinsu ta hanyar fyade suka bayyana a Kotu domin bayar da shaida.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kotu ta daure kasurgumin mai fyade rai da rai sau 7 da shekara 300 a Kurkuku Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama