Birnin kebbi: Dansanda ya harbi saurayi bisa tsautsayi garin ceton barawon babur a cikin Asibiti


Wani dansanda ya harbi wani saurayi garin kokarin ceton ran wani da ake zargi da satan Babur a Asibitin Sir Yahaya da ke garin Birnin kebbi da ke jihar Kebbi ta tsakiya a tarayyar Najeriya.

A wata takarda da ta fito daga Shelkwatar yansandan jihar Kebbi ta hannun Kakakin hukumar yansandan jihar DSP Nafiu Abubakar ranar 24 ga watan Nuwamba ta ce 

" Yansanda sun sami labarin cewa wani mutum mai shekara 35 Abdulazeez Umar ya saci babur a Asibitin Sir Yahaya a garin Birnin kebbi, sakamakon haka fusatattun yan Acaba suka yi kokarin kashe shi,  Yansanda suka garzaya da gaggawa zuwa wajen. Sai dai garin kokarin ceton barawon, sai tsautsayi ya auku wani dansanda mai suna Cpl Sa'adu Adamu ya harbi Habibu Muhammed mai shekara 25 daga karamar hukumar Birnin kebbi".

"Sakamakon haka aka garzaya da Habibu zuwa Asibitin koyarwa na Jami'an Usman Danfodiyo da ke Sokoto inda yake samun kulawan Likitoci. Yayin da aka kama dansanda da ya yi harbi aka tsare shi a sashen kwararrun yansanda masu binciken kwakwaf na sashen SCIID."

A gefe daya kuwa, Gwamnan jihara Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya je wajen da lamarin ya faru, kuma ya kwantar wa jama'a hankali da lallashinsu. Ya kuma yi alkawarin cewa zai biya kudin jinyar wanda aka harba  da ke Asibiti .

Kwamishinan yansandan jihar Kebbi CP Agunbiade Oluyemi Lasore, ya bukaci jama'ar jihar Kebbi su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda kamar yadda suka saba. Ya ce za a tabbatar da an yi adalci da zar an kammala bincike.

SANARWA

IDAN KANA ZAUNE A GARIN BIRNIN KEBBI KO KEWAYE KUMA KANA SON KA SAYAR DA HAJAR KA, WAYA, TALABIJIN, NA URA KO WANI ABU. ZA MU TALLATA MAKA, MU NEMO MAKA MAI SAYE,  GA MAI SAYE GA MAI SAYARWA. KA TUNTUBE MU A OFISHIN MU NA TAUSHI PLAZA, TITIN AHMADU BELLO A GARIN BIRNIN KEBBI.

Arewa Youth Forum (AYF)

Read more at: https://www.vanguardngr.com/2020/11/arewa-youths-want-senator-ndume-out-of-prison/?utm_source=dlvr.it&utm_medium=twitter


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN