Fusatattun matasa a garin Daudu na jihar Benue sun banka wuta a wani Mujami'a Divine Shadow Church,mallakin Malamin addini Joshua Uhembe ranar Talata 3 ga watan Nuwamba bayan sun zarge shi da kitsa sace Mazakutar maza a karamar hukumar Guma.
Wannan yana faruwa ne kwana uku bayan matasa a garin Guma sun yi zanga zanga dangane da zargin bacewar mazakutan mutane a garin.
Kazalika matasan sun zargi Malamin addini Uhembe da shugaban Mujami'an Noah Saka da sace mazakutar matasa bakwai a garin Daudu.
Sai dai wata majiya ta sada zumunta ta ce Malamin addini Uhembe bai halarci taron da Dattijan garin suka shirya kan lamarin ba, sakamakon haka matasa suka harzuka suka banka wa Mujami'ansa wuta.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari