Yadda matsafa suka kashe suka gundule kan mahaifi mai shekara 43 don tsafi


Wasu da ake zargin matsafa ne sun kashe wani mai gadi dan shekar 43 kuma suka gundule kansa a cikin al'umman Oka-Akoko shelkwatar karamar hukumar Akoko ta yamma a jihar Ondo.

Wanda aka kashe mai suna Rotimi Olukoju, yana aiki da wani Banki ne kafin mutuwarsa tranar Alhamis 29 ga watan Oktoba da yamma bayan an uar da gawarsa a gefen hanya a cikin daji.

Wasu kauyawa sun ce an kashe Olokoju a kan hanyarshi ce ta zuwa gona a yankin Iwaro da ke Oko-Akoko, kuma aka cire wasu sassan jikinsa.

Wani dagacikin zuri'ar mamacin ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Juma'a, ya ce yan sanda su kai gawar Olukoju dakin ajiye gawa.

Ya ce mamain ya fara aiki an Bankin ne domin ya sami abin rufa wa iyalinsa asiri kafin ya sami ajalinsa a hannun matsafa.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN