Yadda matasa suka kashe safeton yansanda suka yanke mazakutarsa suka kone ofishin yansanda


Kwamishinan yansandan jihar Ebonyi Philip Maku, ya bayyana yadda wasu bata gari suka yi wa Safeton dansanda mai suna Egu Omini kisar gilla kuma suka yanke mazakutarsa. 

Idan baku manta ba, fusatattun matasa sun farmaki ofishin yansanda na Central Plice station a Abakaliki, suka banka wa ofishin wuta kuma suka kona motoci, babura da Keke Napep da ke harabar ofishin ranar Litinin 27 ga watan Oktoba.

Kwamishinana ya ce bata garin sun kona motocin yansanda kuma sun dauke bindigar Safeto Egu suka tafi da ita.

Ya kuma yi tur da Allah wadai da aikata wannan aiki. Kazalika ya sha alwashin kama wadanda suka jagoranci wannan danyen aiki tare da hukunta su a gaban kuliya.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN