Yadda aka sace wa yaro Almajiri kwanon roban kunu a kasuwar Birnin kebbi


Da tsakiyar ranar Juma'a 16 ga watan Oktoba bayan Sallar La'asar, wani abin tausayi ya auku daga waje, a babban kasuwan garin Birnin kebbi, domin dai an sace wa wani karamin yaro Almajiri kwanon roban kunu da ya sha ya ragesai barci ya kwashe shi.

Bayan Almajirin wanda dan kimanin shekara shida ne ya tashi daga barci, sai jama'a suka lura yana ta neman wani abu da ya bace masa, amma wani bawan Allah da ke sana'a kusa da wajen da yaron ya kwanta, ya lura cewa, yaron ya zo da kwanon roba na kunu, kuma ya dan kurba ya aje saura a gefensa sai barci ya kwashe shi.

Amma bayan ya farka ne sai bai gan kwanon roban ba domin dai bisa ga dukkan alama wani Almajiri, ko yaro mabukacin kunun ya dauke kwanon roban kunun ya yi awon gaba da shi ba tare da jama'a sun lura ba.

Wajen da Almajirin ya kwanta ya yi barci

 

DARASI

Wannan manuniya ne ga babban ibtila'in alamun yunwa da ke addaban wasu bayin Allah a cikin al'kumma, yayin da wadanda ya kamata su taimaka suka kasa samun isar da nasu taimako ga mabukata.

Idan dai har za a iya yi wa dan karamin yaro kuma Almajiri satar kwanon kunu da rana tsaka, wannan ya rage ga mai karatu ya yi hukunci bisa hikimarsa na fahimtar lamurran yau da gobe.

A wani zance kuwa, bayanai sun nuna cewa wasu barayi sun shiga gidan wani bawan Allah a garin Birnin kebbi, amma suka sace hatta rabin buhun shinkafa da ake amfani da shi a gidan, tare da dafaffen shinkafa da aka ci aka rage a kwano, bayan sandan burodi da wani ya saya domin a yi wa yaransa shayi da safe.

Haka zalika rahotu ya nuna cewa hatta tukunyan miya da nama a ciki a saba sacewa a gidajen bayin Allah.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN