Safeto Johnson Samanja ya harbe wani saurayi mai suna Samuel Jonathan dan shekara 19 mai sanar'ar askin Barber, bayan ya kwankwadi barasa a gidan giya.
Rahotanni sun ce Safeton ya yi harbi da bindiga a cikin iska, amma sai jama'a suka bukaci ya daina domin gudun tsautsayi. Gogan yaki sauraron jama'a, sai ya sake harba bindiga karo na biyu, nan take harsashi ya je ya sami saurayin a kirji kuma ya fadi nan take.
An garzaya zuwa Asibiti dasaurayin, amma Likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Hakimin unguwar mai suna Ishaya Babowa, ya shaida wa City News cewa tun farko a ranar, an jiyo Safeton yana barazanar cewa yau zai kashe mutum daya ko biyu, duk da yake shi kansa Safeton yana zaune a Dutsen Alhaji.
Wasu fusatattun matasa sun je gidan sayar da barasa da Safeton ya sha giya, suka aikata barna bisa zargin cewa masu gidan giyan sun kasa nuna damuwa bisa abin da Safeton ya aikata. Daga bisani suka toshe mashigar unguwar kafin yansanda daga Apo su tarwatsa su.
Haka zalika rahotanni sun ce yansanda sun ceci Safeton daga hannun fusatattun matasan suka tafi da shi ofishin yansanda da ke Apo a birnin Abuja.
Kakakin yansandan birnin Abuja ASP Mariam
Yusuf, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce an kama dansandan da ya yi kisan kuma har an gana da iyalan saurayin da aka halaka.
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/
Rubuta ra ayin ka