Rikicin APC na cikin gida: Marafa ya nufi kotun koli a kan taron jam'iyya


Rikicin cikin jam'iyyar APC ta jihar Zamfara na cigaba da aukuwa tsakanin bangarorin guda biyu, wanda har kotu bata gama hukunci akai ba, Legit.ng ta wallafa. Bangare daya na jam'iyyar, wanda Sanata Kabiru Marafa ke jagoranta sun ce za su daukaka kara zuwa kotun koli akan hukuncin da kotun daukaka kara ta Sokoto tayi akan taron jam'iyyar.

Kamar yadda kotun daukaka kara ta Sokoto ta tabbatar kuma ta gamsu da hukuncin da taron nadin shugabannin jam'iyyar da akayi a ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoba, wadda Alhaji Lawal Liman ya jagoranta. Kotun daukaka karar ta Sokoto ta yanke hukuncin da babbar Kotun Zamfara, wacce ta rushe duk nadin da taron yayi.

Bakyasuwa yace bangaren da Marafa ke jagoranta basu amince da hukuncin kotun daukaka karar ba. Yace don kawai tsohon Gwamna Abdulaziz Abubakar Yari na jagorantar dayan bangaren baya nufin sune za su nada shugabannin Jam'iyyar. Ya kuma zargi shugabannin Jam'iyyar APC na kasa akan mara wa bangare daya baya, da nuna son kai wurin hukunci.

Yace bangarensu na bukatar hukuncin gaskiya da gaskiya. A wani labari na daban, daliban jami'o'i karkashin inuwar kungiyar daliban jami'o'i ta kasa ta ce hakurinsu ya kare sakamakon dogon yajin aikin da kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i suka fada.

Daliban sun ce za su nuna rashin jin dadinsu a kan yadda yajin aikin ke tsawaita a ranar Talata. Sun ce za su fara zanga-zangar ne ta gaban katafaren ginin majalisar tarayya sannan su wuce zuwa ofishin ma'aikatar ilimi daga nan su garzarya zuwa ma'aikatar kwadago da aikin yi.

Source: LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN