Buhari ya aika muhimmin sako zuwa rundunar 'yan sanda a kan ma su zanga-zanga


Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya umarci babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, da ya tabbatar da tsaron lafiyar ma su zanga-zangar lumana ta neman a kawo karshen rundunar SARS.

Kazalika, shugaba Buhari ya jaddada cewa matasan na da ikon bayyana rashin gamsuwarsu ta hanyar gudanar da zanga-zangar lumana. Sai dai, shugaba ya yi kira ga matasan a kan su bawa gwamnati lokaci domin duba bukatunsu da tuni aka kafa kwamiti na musamman domin yin hakanMinistan harkokin matasa da wasanni, Sunday Dare, ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala ganawa da shugaba Buhari a Villa.

Ministan ya ziyarci shugaba Buhari ne domin yi masa cikakken bayani a kan zanga-zangar da ta kara karfi ranar Litinin. A cewar, Dare, shugaba Buhari ya sanar da shi cewa shine uba wurin dukkan matasan kasar nan, kuma ba zai so wani abu ya cutar dasu ba Shugaba Buhari ya ce alhakinsa ne ya kare matasa masu zanga-zanga daga cin zalin 'yan sanda.

Dare ya ce shugaba Buhari ya bashi tabbacin cewa ya saurari korafin matasan kuma zai share musu hawaye. Ministan ya ce ya gabatar da jawabi ga Buhari a gaban shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, kamar yadda jaridar The Sun ta rawaito.

Source: LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN