Wani Kare da ke gida halittar Rottweiler, ya cije wani Jariri da aka haifa kwana daya bayan haihuwarsa a Duniya sakamakon haka ya mutu a birnin Hamilton a kasar New Zealand ranar Lahadi 25 ga watan Oktoba.
An garzaya zuwa Asibiti da Jaririn, amma Likitoci suka ayyaana cewa ya mutu sakamakon cizo da Karen ya yi masa a wurare da dama.
Wata makwabciyar gida da lamarin ya faru, ta gaya wa wani shafin labarai na yanar gizo cewa " Na ga mahaifiyar jaririn tana rike da shi a gefen titi,. Amma Karen ya cije Jaririn ne lokacin da mahaifiyarsa ta shiga dakin wanka".
Ta kara da cewa " Karen Rottweiler, ya yi kokarin binne Jaririn ta hanyar tona rami da kafafunsa"
Kazalika ta ce mahukunta sun kwace Karen Rottweiler da wani Kare da mahaifiyar Jaririn take zaune da su a gidan kuma suka tafi da su.
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari