• Labaran yau


  An kama mutum hudu da sukan tone kabari suka sare kan gawa don tsafi a jihar Niger


  Yansandan jihar Niger sun kama mutum hudu da Kwarangwam kan dan adam bisa zargin tsafi a Kauyen Sabon Pegi da ke jihar ranar 3 ga watan Oktoba.

  Kakakin yan sandan jihar Niger Abidoun Wasiu, ya ce wadanda aka kama su ne Alhaji Suleiman Abubakar mai shekara 50, Babuga Mamman  dan shekar 42yrs, Abdullahi Dogo mai shekara 30 da Abubakar Abdullahi dan shekara 31, dukkansu yan Kauyen  Sabon Pegi a karamar hukumar Mashegu.

  Kakakin yansanda Wasiu,ya ce binciken farko ya nuna cewa wadanda aka kama sun tone Kabari kuma suka sare kan Gawa da aka binne a Makabartar Kauyen Kanti a karamar hukumar Ibbi Mashegu ranar 3 ga watan Oktoba da karfe 8 na dare.

  Ya ce wadanda aka kama sun gaya wa yansanda lokacin bincike cewa, wani mai suna Nasiru dan garin Koko a jihar Kebbi, da Muhammadu  dan garin Sabon Pegin ne suka yi alkawarin cewa zasu basu Naira Miliyan biyu idan suka samo masu kan dan adam.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kama mutum hudu da sukan tone kabari suka sare kan gawa don tsafi a jihar Niger Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama