• Labaran yau


  Zaben Edo: An kafa kotun sauraron korafe korafen zabe daga APC da sauran jam'iyyu


  Yan kwanaki bayan kaddamar da Godwin Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Edo, shugabar kotun daukaka kara, Justis Monica Dongban-Menem ta kafa kotun sauraron karar zabe domin duba kararrakin da zai fito daga zaben.


  A cewar jaridar The Nation, an tsara zaman sauraron kararrakin zaben a harabar babbar kotun da ke Benin, babbar birnin jihar Edo. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren kotun zaben, Sunday Martins ya fitar a ranar Talata, 22 ga watan Satumba.


  “Ana sanar da jama’a cewa mai girma shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya, Justis M. B Dongban Mensem ta kafa kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan da aka gudanar a jihar Edo.” Jawabin ya ci gaba da bayyana cewa shugaban alkalai na jihar Edo, Justis Edigin ya amince da amfani da dakin sauraron kararrakin zabe da ke harabar babbar kotu a Sapele Road, birnin Benin don sauraron korafe-korafen.


  Legit.ng ta tuna cewa Obaseki na PDP ya kayar da Ize-Iyamu na APC a zaben. Sai dai Ize-Iyamu wanda yace har yanzu yana nazarin sakamakon zaben ne bai bayyana ko zai kalubalanci sakamakon ba a kotu.Da wannan shahadar, Obaseki da Shaibu sun cika sharrudan dokar zabe domin rantsar da su ranar 12 ga Nuwamba, 2020 a Benin City domin wa'adinsu na biyu a ofis.

  Source: Legit  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Zaben Edo: An kafa kotun sauraron korafe korafen zabe daga APC da sauran jam'iyyu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama