• Labaran yau


  Yanzu yanzu: Jam'iyar APC ta dakatar da Gwamna Fayemi daga jam'iyar a jihar Ekiti

   


   Kwamitin zartarwa na jam'iyar APC a jihar Ekiti, ta dakatar da Gwamna Kayode Fayemi daga jam'iyar.


  A wata sanarwa da jam'iyar APC ta fitar ranar Juma'a 25 ga watan Satumba, ta yi zargin cewa ta dakatar da Gwamnan ne sakamakon " Ayyukan cin amanar jam'iyar musamman irin rawa da ya taka lokacin zaben Gwamnan jihar Edo da aka kammala kwanan nan".

   

  Haka zalika takardar ta yi zargin cewa "Kwanaki biyar kafin zaben jihar Edo, Gwamna Fayemi ya ba wani jigo a jam'iyar PDP, Femi Kayode masauki a fadar Gwamnatin jihar Ekiti, da ke Ado Ekiti, kuma suka kitsa yadda za a gudanar da Juyin mulki akan jam'iyar APC a jihar Edo.

   

  Gwamna Fayemi ya kuma taka rawa wajen ganin jam'liyar APC ta sha kasa a zaben Gwamnan jihar Oyo". Kamar yadda takardar ta sanar.

   


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yanzu yanzu: Jam'iyar APC ta dakatar da Gwamna Fayemi daga jam'iyar a jihar Ekiti Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama