Minista Sadiya Umar Farouq Ta Auri Iya Mashal Sadique?

 


Yayin da kafafen yada labaran Najeriya ke ci gaba da yada labaran yiwuwar Minista Sadiya Umar Farouq ta auri Air Marshal Sadique, jama'ar gari kuma na ta fassara abin da hankulansu ke nuna masu.

Kafafen yada labarai a Najeriya na ta yamadidin cewa Babban Hafsan Hafsoshin saman kasar, Air Marshall Sadique Abubakar ya angwance da Ministar Harkokin jinkai Sadiya Umar Farouq.

Jaridar Daily Trust ta ce tabbatattun bayanai na nuna cewa Babban Hafsan lalle ya auri Ministar ranar jummu'a 18/09/20, inda aka daura auren a wani masallacin dake unguwar manya wato, Maitama dake Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja.

Kodayake Babban Hafsan da kuma Ministar duka ba wanda ya ce kome akan batun.

Bnciken da wakilinmu yayi a hedikwatar sojojin Najeriya da ma makusantan Ministar dukkanninsu sun ce basu san kome akan wannan labarin ba.


 

Wakilinmu ya kuma tuntubi wani babban abokin Babban Hafsan wanda ya ce shi ma ya tambayi abokin nasa amma ya ce mai labatin shiririta ne.

Mai sharhi kan al'amuran zamantakewa, Mohammed I. Usman ya ce kodayake babu wani abin mamaki in har wannan aure ya tabbata, to amma ganin Habban Hafsan ya yi watsi da maganar lokacin da abokansa suka tuntubeshi to ai karshen zance kenan.

Komadai menene gaskiyar wannam batu, lokaci ka iya bayyanawa.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina ta sauti:

  
 Source: VOA
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN