Matata ta yaudare ni na siya babur daga hannun kwartonta: Magidanci ya fada wa kotu


Isaac Ayodele wani tsohon ma'aikacin banki, a ranar Alhamis ya shaida wa alƙalin kotun gargajiya da ke a Mapo Ibadan cewa matarsa Omotayo ta yaudare shi ya siya babur daga hannun kwartonta. Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ta ruwaito cewa Ayodele ya kuma fada wa kotu cewa matarsa tana cin amanarsa na aure. "Na ce matata ta dena aiki bayan na samu aiki.


Amma daga baya sai na rasa aiki na sai na ƙyalle ta ta fara sayar da abinci daga nan ta fara bin maza. "Ina son sake sabuwar rayuwa sai Omotayo ta haɗa ni da kwarton ta a matsayin sai sayar da babur da zai amince in riƙa biyan kuɗin a lokaci zuwa lokaci. "A lokacin da na gano abinda suke yi, ita da kwarton ta sun yi barazanar za su kashe ni. "Ta kwashe kayan ta daga gida na daga baya ta kwashe yaran mu," in ji shi.


Matarsa, Omotayo a bangarenta ta ce ta shigar da ƙarar ne domin ta tsira da ranta. A cewar ta Ayodele mutumin banza ne da ke dukan ta duk lokacin da ta nemi taimakon kudi daga hannunsa. "Miji na mugu ne kuma baya nufi na da alheri. Ya hana ni aiki ya kuma ƙi kula da ni da yara na. "Du k lokacin da na tambaye shi kuɗi sai ya doke ni.


Bayan an kore shi daga aiki mai gidan hayar mu ya tashe mu sai yaya na ya kama min gidan haya. "Na nemo masa babur ya siya amma ya ƙi cika alƙawari. Mai babur ɗin ya kira ƴan sanda sun kama ni," in ji Omotayo. Alƙalin kotun ya bukaci su kawo hujjoji game da zargin da suka yi wa juna ya kuma dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 13 da watan Oktoba. Bale ya roki wannan alfarman daga hannun kotu ne cikin takardar neman raba aure da ya shigar a kotun.

Source: LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN