Ka san dalilin shanyewar ƙafa bayan allura a ɗuwawu?


 

"Injection Nerve Palsy" matsala ce da ke faruwa sakamakon raunata jijiyar laka ta 'sciatic nerve' da ke kai saƙonni zuwa wasu gungun tsokokin ƙafa.

Wannan matsala na faruwa ne idan aka kuskure aka tsira allura a kan jijiyar yayin yin allura a ɗuwawu, ko idan ruwan allurar ya lalace, ko kuma idan allurar ko ruwan allurar ya kawo kumburi a kewayen jijiyar wanda hakan ka iya danne ko shaƙe jijiyar har aikinta ya kassare.

Waɗanda suke da haɗarin gamuwa da wannan matsala sun haɗa da:

1) Wanda bai ba da haɗin kai yadda ya kamata ba yayin yin allurar, musamman ƙananan yara.

2) Mai rama sosai.

3) Faɗawa hannun wanda bai ƙware ba.

4) Da kuma wanda tsautsayi ya faɗawa.

Alamomin wannan matsala na faruwa ne a dukkan rassan jijiyar a ƙafar nan take ko bayan wani ɗan lokaci.

Alamomin sun haɗa da:

1) Matsanancin ciwo,

2) Sagewa,

3) Rauni ko rashin ƙarfin ƙafar,

4) Rashin ji a fata idan aka taɓa,

5) Wahalar tafiya: ɗingishi, jan ƙafa, da sauransu.

Da zarar an lura da waɗannan matsaloli da aka ambata a sama, a gaggauta sanar da jami'in lafiyar da ya yi allurar domin ɗaukar matakan gaggawa. Wannan matsala ana warkewa kamar ba a yi ba. Sai dai jinkirin zuwa asibiti na iya kawo naƙasu ga ƙafar.

Saboda haka, akwai buƙatar ganin likitocin fisiyo (Physiotherapists) da ke kula da matsalolin jijiya, ƙashi, da tsoka domin sune ke da alhakin farfaɗo da aikin ƙafar.

Source: Physio Hausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN