Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya kaddamar da allurar rigakafin cutar haukar Kare kyauta a fadin jihar Kebbi a garin Birnin kebbi ranar Litinin.
Wannan ya zo daidai da ranar cutar haukan Kare na duniya wanda aka gudanar ranar Litinin 28 ga watan Satumba a babban dakin taro na shugaban kasa da ke Birnin kebbi.
Gwamna Bagudu ya ce cutar haukan Kare ana iya daukarta daga Kare, ya kalubalanci masana lafiyan dabbobi su samar da magani da kuma rigakafin cutar domin a kawar da ita gaba daya.
Kawmishinan lafiyar dabbobi da albarkatun kifi na jihar Kebbi Alhaji Aminu Garba Dandiga, ya ce Ma'aikatarsa karkashin Gwamnatin jihar Kebbi ta yi wa Karnuka 17,200 rigakafin cutar Kare, daga cikin adadin Karnuka 40,000 da ake da su a fadin jihar Kebbi.
Shugaban majalisar harkokin kula da lafiyar dabbobi na Najeriya AIG, Aishatu Ababakar-Baju, ta ce dubban mutane da dabbobi ne ke mutuwa a fadin Duniya a kullum, sakamakon cutar haukan dabbobi, duk da cewa ana iya yin rigakafin cutar kaso 100 domin kauce wa kamuwa da cutar.
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/