Wasu ‘yanzanda bisa rakiyar ‘yan ta’adda a kasar Kongo sun kwacewa ofishin jakadancin Najeriya dake kasar wani gini inda suka kori ma’aikatan ciki da kuma kwace musu kayan amfaninsu.
Ma’aikatan Ofishin jakadancin Najeriya a kasar na cikin gidan inda wata mata me suna Hajiya Khadija bisa rakiyar ‘yansanda da wasu ‘yan daba suka shiga gidan da wata takardar Kotu suka kori daya daga cikin ma’aikacin ofishin jakadancin Najeeiyar me suna Kazeem suka kuma kwace masa kayan aikinsa, zuwa yanzu dai a Ofishinsa yake bacci, kamar yanda Sahara Reporters ta bayyana.
Iyalan Jean Claude Okito dake kasar sun yi ikirarin cewa Najeriya na amfani da ginin wanda mallakinsu ne ba bisa ka’ida ba.John Obi wanda shugaban ‘yan Najeriya ne dake zaune a kasar Congo yace wannan abin kunyane ga Najeriya inda ya nemi majalisa ta gayyaci Ministan harkokin kasashen waje dan jin ba’asi akan lamarin.
hutudole
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/