Bayan karɓar N5m: Yan bindiga sun kashe jami'in DSS a jihar Katsina


Masu garkuwa da mutane sun kashe wani jami’in hukumar tsaro na farin kaya mai shekaru 33, Sadiq Abdullahi Bindawa, bayan sun karbi naira miliyan 5 a matsayin kudin fansa. An yi garkuwa da marigayin, wanda ya ke aiki da sashin leken asiri na hukumar da ke Abuja, a ranar Asabar a gidansa da ke bayan sakatariyar tarayya a birnin Katsina.A cewar majiyoyi abun dogaro, Marigayi Bindawa tare da dansa mai shekaru hudu, sun je Katsina a ranar Juma’ar da ta gabata domin yin hutun karshen mako tare da yan uwansu lokacin da wannan mummunan al’amari ya afku. Makasan sun kai farmaki gidan marigayin da misalin karfe 10:30 na rana sannan suka tsere dashi zuwa wani wuri da ba a sani ba. Wani dan uwansa, wanda ya nemi a boye sunansa, ya fada ma jaridar Thisday a ranar Talata cewa yan bindigan sun nemi a biya fansa sa’o’i 48 bayan sun sace shi.Majiyin ya ce da fari masu garkuwan sun bukaci a biya naira miliyan 13 kudin fansa, amma bayan rokonsu da aka yi da tattaunawa, sai suka yarda a biya naira miliyan 5 domin su sake shi. Ya ce: “Yana shirin shiga gidansa da ke bayan sakatariyar tarayya a daren ranar Asabar da misalin karfe 10:30 na dare bayan ya dawo daga babban gidanmu lokacin da masu garkuwan suka futo dashi daga mota ta karfi, bayan sun yi wa mai tsaron shi duka na fitar hankali. 


 Mun kai rahoton lamarin ga ofishin yan sandan Batagarawa amma babu abunda aka yi. “A ranar Lahadi sai yan bindigan suka kira ta wayarsa sannan suka bukaci a biyar naira miliyan 13 a matsayin kudin fansa kafin su sake shi, amma bayan an roke su sai suka amince a biya naira miliyan 5 sannan suka bukaci mu hadu dasu a Charanchi mu basu kudin. “Mun kai masu naira miliyan biyar din a ranar Lahadi a Charanci kamar yadda muka yi yarjejeniya, sai suka ce mu je mu karbe shi a garin Kurfi a safiyar ranar Litinin.Amma da muka kai wajen, sai muka tarar da gawansa dauke da harbin bindiga a kansa, kunnuwansa da bayansa. Mun binne shi a jiya (Litinin).” Rundunar yan sandan Katsina bata ce komai ba a daidai lokacin kawo wannan rahotonHukumar tsaro na farin kaya (DSS) ta gayyaci Mailafia a watan Agusta kan ikirarinsa na cewa wani gwamnan arewa ne shugaban Boko Haram.

Source: Legit
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN