• Labaran yau


  Bani da shaida kan ikirarin da na yi - Obadiah Mailafiya  Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Obadiah Mailafiya ya bayyana cewa bashi da Hujjar da zai iya bayarwa kannikirarin da yayi.Ya bayyana hakane a ranar Litinin biyo bayan gayyatar da DSS suka masa zuwa Ofishinsu. 

   

  Yace baida hujjar da zai iya bayarwa kan zargin da yayi cewa akwai hannun gwamnati a kashe-kashen da ake yi a Najeriya.Ya dai yi zargin cewa akwai kwamandan Boko Haram da Gwamnan Arewa ne, wanda hakane tasa DSS din suka gayyaceshi har sau 3.

   

  Bayan ganawa da DSS din da yayi a yau yace an karramashi lokacin ganawar kuma babu wani cin zarafi da aka masa, yace amma da zai samu dama da ya gyara wancan kalami nashi da yayi a baya.Ya kuma bayyana cewa akwai sanda yaga wasu suka shawagi a kofar gidansa da bai gane musu ba, saidai Katanga ya haura ya tsere saboda yana jin cewa akwai wasu manya dake son kasheshi.

  hutudole


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Bani da shaida kan ikirarin da na yi - Obadiah Mailafiya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama