• Labaran yau


  Ba zamu lamunce cin fuska ga Buhari daga wadanda ya nada a mukamai ba - Ahmad Lawan

  Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmad Lawan , ya yi gargadi ga wadanda shugaba Buhari ya nada su a kan mukamai bayan takun saka da ake samu tsakanin bangarorin zartarwa da na yan Majaalisa, musamman yan makonni da suka gabata.

  Lawan ya yi wa manema labarai wannan bayani ranar Litinin 31 ga watan Agusta, jim kadan bayan shugaba Buhari ya nada Kwamiti kan bangarorin zartarwa da na yan Majalisa, wanda ke samun shugabancin Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

  Ya kara da cewa shuga Biuhari ya yi jawabi kan wannan matsalar. Ya ce bangaren Majalisa za ta yi aiki tukuru, kuma za ta tabbatar bangaren zartarwa bata wuce makadi da rawa ba wajen tafiyar da aikinta.

  Ya kuma yi kira ga yan jam'iyar APC da aka zaba a mukamai daban daban su ci gaba da tabbatar da cewa, sun cika alkawari da suka yi wa jama'arsu lokacin yakin yeman zabe, domin kare martaba da mutuncin jam'iyar.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ba zamu lamunce cin fuska ga Buhari daga wadanda ya nada a mukamai ba - Ahmad Lawan Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama