• Labaran yau


  An kashe King K.I fitaccen mai flashin wayar salula a Birnin kebbi

  A cikin daren Litinin 14 ga watan Satumba, an shiga gidan King Izeak wanda ake wa lakabi da K.I Flashing kuma aka yi ta caka masa wuka a kai da jikinsa.

  Lamarin ya faru ne a unguwar Badariya da ke garin Birnin kebbi. Sakamakon raunuka da ya samu, K.I Flashing ya mutu da sanyin safiyar Laraba 16 ga watan Satumba.

  Mujallar ISYAKU.COM ya gano cewa makwabta sun sanar da yansanda domin fara bincike kan lamarim.

  K.I fitaccen masanin ingizon sila-silar aikatau na wayar salula ne, mai shagunan wasan PS a Taushi plaza, kuma Malamin makarantar Sakandare na Junju a garin Birnin kebbi.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kashe King K.I fitaccen mai flashin wayar salula a Birnin kebbi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama