Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana haka ne cikin wata hira da ya yi da BBC.
Gwamnan ya ce ya kamata mulki ya koma kudancin kasar a shekarar 2023 bayan wa'adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.
"Ana
cewa ina son shugabancin kasa tun ina minista na FCT [Babban Birnin
Tarayyar Najeriya]. Wannan shirme ne. Ba na so [Shugabancin Najeriya.
Allah shi yake ba da mulki, ko kana so ko ba ka so idan yana so zai ba
ka amma ni ban taba neman shugabancin Najeriya, ba wanda zai ce na taba
nema," in ji Gwamna El-Rufai.
Ya
kuma ce, "A siyasar da ake yi a Najeriya, akwai tsarin da ake bi na
karba-karba, inda kowa ya amince cewa idan arewa ta yi mulki shekara
takwas, kudu za ta yi mulki shekara takwas."
Ya ce duk da ba a rubuta tsarin karɓa-karɓan a tsarin mulki ba, amma kowane ɗan siyasa a ƙasar ya san da shi.
"Shi
ya sa na fito na ce bayan Shugaba Buhari ya yi shekara takwas, ka da
wani ɗan arewa ya nemi muƙamin. A bar ƴan kudu suma su sami shekara
takwas."
Ya ce shi karan kansa cancanta yake bi wurin bai wa mutu aiki.
Batun rufe kasuwannin Kaduna
Tun
da cutar korona ta bayyana a Najeriya, gwamnatoci sun ɗauki matakan
killace al'umominsu a gida inda har ta kai sun kulle makarantu da
wuraren aiki da kasuwanni.
A
jihar Kaduna, duk da gwamnatin jihar kaduna ta sassauta matakan kullen
da ta saka wa al'umar jihar, har yanzu ba ta buɗe wuraren ibada da
kasuwanni da makarantu ba.
Wannan ne ya sa ƴan kasuwa ke ƙorafe-ƙorafe kan batun, suna cewa matakin gwamnan jihar na iya kassara su.
Amma gwamnan na Kaduna ya kare kansa daga zargin da ake yi cewa ya ƙi tausaya wa ƴan kasuwan.
"Su ƴan kasuwa suna cewa sun fara bara. Mun ji, amma gara kayi bara kana da rai da ka mutu."
Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta buɗe kasuwanni da wuraren ibada ne kawai bayan ta sha ƙarfin annobar.
Mallam
Nasiru El-Rufai: "Bayan rufe jiha da muka yi kwana 75, sannu a hankali
mun buɗe wasu sassan na rayuwa domin mu ga ko mutane za su yi biyayya ga
dokokin da jami'an kiwon lafiya suka gindaya domin kare al'umma daga
kamuwa da cutar ta korona."
Ya koka da yadda mutane a jihar ba sa kiyaye wa kamar yadda aka buƙace su.
"Idan
muka buɗe masallatai da kasuwanni, cunkoson da muke gani ana yi ƙaruwa
zai yi ba raguwa ba. Kuma mutum ɗaya da ke da cutar na iya yaɗa ta ga
dubban mutane."
Ya kuma ce saboda yadda cutar ke kara bazuwa a jihar, gwamnati na iya mayar da hannun agogo baya.
"Yanzu ma abin da muke dubawa shi ne, ƙila mu rufe jihar domin yadda cutar ke ƙaruwa.
Muna fargabar yana iya fin ƙarfin asibitocinmu. Ƙila su sake rufe jihar a koma gidan jiya."
Ya
kuma yi alƙawarin tallafa wa ƴan kasuwan idan komai ya koma dai-dai:
"Za mu sami hanyoyin tallafa mu su bayan komai ya lafa, amma mutumin da
ya riga ya mutu, ko wace irin kasuwanci yake yi ba zai amfane shi ba,
sai dai ta lahira."
Yaushe za a buɗe makarantu?
Duk
da gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da ranakun da za a buɗe
makarantu a ƙasar, gwamnan na Kaduna na ganin akwai sauran rina a kaba.
Ya ce gwamantinsa za ta yi nazari domin ta ga ko ya dace a sake buɗe makarantu a faɗin jihar:
"Muna nan muna dubawa. Akwai manyan shirye-shirye da za mu yi - idan ba haka ba, ba za mu buɗe su ba," inji gwamnan.
Matsalar tsaro a kudancin Kaduna
Wani batu da ke jan hankalin mutane a Najeriya shi ne na rashin tsaro.
Yayin
da jihohin arewa maso gabas ke fama da ayyuakn ta'addanci, su kuwa na
arewa maso yammaci na fuskantar barazana ne daga ɓarayin daji da kuma
masu satar mutane domin su karɓi kuɗin fansa.
Gwamna
El-Rufai ya ce ƴan bindigan da ke kai hare-hare a kudancin jihar suna
yin haka ne domin dalilai na tattalin arziki: Waɗannan ƴan bindiga su ne
ke kashe-kashe da sace-sace a kudancin Kaduna."
Ya kara da cewa, "abin da na lura shi ne wasu mutane na amfani da siyasa da addini ko ƙabilanci a dagula maganar."
Da BBC ta tambaye shi su wane ne ke amfani da siyasa da addini, sai gwamnan ya ce:
"Akwai
waɗanda mun kayar da su a zaɓe amma har yanzu sun kasa dangana, shi
yasa suke son tayar da hankali. Sun rantse sai jihar nan an kasa
mulkinta."
Ya kuma ce akwai wasu kuma da suka kafa gaba da wasu al'umomin da ke zaune cikin jihar, har suna kiransu baƙi.
Ya
ce akwai garuruwa kamar Zonkwa da Kafanchan da Zangon-Kataf da garuruwa
da mutane daga wasu yankunan arewacin Najeriya kamar Kano da Bauchi da
sauransu sun je kudancin Kaduna sun zauna.
"Akwai
waɗanda suka tashi suna cewa waɗannan mutanen baƙi ne kuma sai sun bar
wurin. An fara irin wannan tashin hankalin a jihar Kaduna tun 1980 da
aka far wa mutanen Kasuwan Magani aka kashe mutum 11."
Mallam
Nasiru El-Rufai ya kare zargin da ake wa gwamnatinsa cewa ta kasa
magance matsalar, inda ya ce ko a zamanin tsohon gwamna marigayi Patrick
Yakowa irin wannan rikicin ya auku.
"Patrick Yakowa ɗan kudancin Kaduna ne, kuma mutanen yankin sun nuna irin wannan hali. Sun far wa mutane kuma sun kashe su."
Ya kuma ce saboda matakan tsaron da ya riƙa ɗauka ne lamarin tsaron ya tsaya inda yake.
"Wadanda
ke cewa abin ya fi ƙarfinmu ba su yi mana adalci ba. Abin da mutane ba
su sani ba shi ne yadda muka hana ƙulle-ƙullen da wasu ke yi na far wa
mutane su kashe su a jihar."
Rahotu daga shafin BBC
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/